
Kungiyar ‘yan asalin Ebonyi mazauna ketare (AEISCID) ta yi gargadi ga Sanata Onyekachi Nwebonyi, mai wakiltar mazabar Ebonyi ta Arewa a majalisar dattawa, bisa kalamansa da suka shafi rikicin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Shugaban kungiyar, Paschal Oluchukwu, ya soki yadda Onyekachi ke kare Sanata Godswill Akpabio ta hanyar cin mutuncin manyan mutane. Kungiyar ta bukaci ’yan mazabar Ebonyi ta Arewa da su fara shirin yi wa Onyekachi kiranye, tana zargin ya zubar da mutuncin jihar.
Oluchukwu ya bayyana halayen sanatan a matsayin rashin kamun kai da rashin ladabi, yana mai cewa hakan na iya jawo wa al’ummar Ebonyi suna.
Kungiyar ta ce tana da niyyar shigar da korafi ga hukumar INEC domin kwace kujerar sanatan. Hakanan, ta bayyana damuwarta kan rade-radin cewa an kulla wata yarjejeniya ta siyasa dangane da zaɓen gwamnan Ebonyi a 2027.
AEISCID ta yi kira ga al’ummar Ebonyi North su fara shirin tsige Sanata Nwebonyi idan ya ci gaba da irin wannan halayen da take kira “barar da mutunci.”