Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Shugabancin NNPP

Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta yi fatali da karar da wasu magoya bayan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso suka shigar, suna kalubalantar halaccin shugabancin jam’iyyar NNPP karkashin Dr. Boniface Aniebonam da Dr. Agbo Major.

Alkalin kotun, M.A. Hassan, ya bayyana cewa kotu ba ta da hurumin tsoma baki a cikin harkokin shugabancin jam’iyya, sai dai idan batun ya shafi takarar zabe. Hukuncin ya tabbatar da cewa bangaren Agbo Major ne ke da ikon shugabantar jam’iyyar, yayin da aka yi watsi da bukatun masu karar.

Hukuncin kotun na jaddada na wata kotu a jihar Abia, wacce ta yarda da cewa kwamitin amintattun jam’iyyar karkashin Dr. Boniface Aniebonam ne ke da cikakken iko. Lauyan wadanda suka shigar da kara, Segun Fiki, ya yaba da hukuncin, yana mai cewa hakan ya tabbatar da sahihancin shugabancin NNPP.

A bangarensu, kakakin yada labarai na tsagin Kwankwaso, Ladipo Johnson, ya bayyana rashin jin dadinsu da hukuncin, yana mai cewa ba a tabbatar da halaccin Agbo Major ba. Ya ce, “Wannan wata dabara ce kawai don karkatar da hankulan jama’a,” kuma sun yi alwashin fitar da sanarwa nan gaba domin bayyana matsayinsu kan hukuncin.

Hukuncin kotun na daga cikin matakan da ke nuna ci gaban shari’a a harkokin siyasa a Najeriya, yayin da jam’iyyar NNPP ke fuskantar sabbin kalubale na shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *