Gwamna Abba Ya Bayyana Dalilin Sake Nada Dr. Aliyu a Matsayin Sarkin Gaya

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana dalilin da ya sa gwamnatinsa ta mayar da Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir a matsayin Sarkin Gaya. Gwamna Abba ya ce an dawo da sarkin ne saboda jajircewarsa, tawali’u, da mika wuya ga hukuncin Allah lokacin da aka tube shi.

A cikin sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Abba ya yaba wa Sarkin Gaya kan yadda ya nuna hakuri da dogaro ga Allah. Ya ce, “Sarkin Gaya ya amshi kaddararsa cikin natsuwa ba tare da nuna adawa ba.”

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa za ta inganta ci gaban masarautar Gaya, tare da tura injiniyoyi domin fara ayyukan raya al’umma a yankin. Ya ce, “Muna da niyyar sauya fasalin Gaya zuwa birni na zamani.”

Dr. Aliyu Abdulkadir ya nuna godiya ga gwamna bisa amincewa da shi, yana mai alwashin yin aiki kafada da kafada da gwamnati domin ci gaban masarautar. Wannan mataki na gwamnan ya jawo yabo daga jama’a, inda suka ce hakan na nuna cewa tawali’u da hakuri na da matukar muhimmanci a shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *