Wike Ya Karyata Rade-radin Lafiyarsa, Ya Ce Yana cikin Koshin Lafiya


Nyesom Wike, ministan Abuja, ya musanta rade-radin da ke cewa ya yanke jiki ya fadi sannan aka garzaya da shi Faransa don neman lafiya. Wike ya bayyana cewa, wannan labarin karya ne da aka kirkira domin jawo rudani ga jama’a.

A yayin da yake duba ayyukan gine-gine a Abuja, Wike ya tabbatar da cewa yana cikin koshin lafiya, yana mai cewa masu yi masa fatan mutuwa za su riga shi barin duniya. Ya yi kira ga mutane da su daina yi wa ‘yan uwansu fata marar kyau, yana mai jaddada cewa Allah ne kadai ke sanin ranar mutuwar kowa.

Wike ya ce, “Duniya ba madauwama ba ce,” kuma ya bayyana cewa ya halarci bukukuwan Sallah tare da manyan shugabanni a Abuja. Ya zargi wadanda suka yada wannan jita-jita da niyyar karkatar da hankalin jama’a daga wasu abubuwan da suka shafi tsaron kasa.

Ministan ya jaddada cewa jita-jita ba za ta hana shi gudanar da ayyukansa ba, yana mai cewa, “Mun saba da irin wadannan sharrin siyasa.” Wike ya yi alkawarin ci gaba da aiki da gaske a Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *