
Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sokoto ya bayyana alhinin sa kan kisan wasu ‘yan Arewa 16 da aka yi a garin Uromi, Jihar Edo. A cikin sanarwa da ya fitar, gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalai da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a wannan mummunan lamari.
Gwamnan ya bukaci hukumomin tsaro da su gaggauta kama wadanda suka aikata wannan kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a. Ya jaddada cewa wannan harin wani babban kalubale ne da ke bukatar martani mai karfi daga hukumomin tsaro, don haka ya bukaci a yi adalci.
Ahmed Aliyu ya bayyana cewa cin zarafi da daukar doka a hannu abin Allah wadai ne a cikin al’umma. Ya kuma kira ga al’ummar kasa da su rungumi zaman lafiya da mutunta juna domin samar da ingantacciyar rayuwa da ci gaban kasa.
A halin yanzu, ana jiran matakan da hukumomi za su dauka kan wannan lamari, tare da fatan ganin an yi adalci domin wanzar da zaman lafiya a Najeriya.