
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa azumin bana ya zo ne a lokacin da al’umma ke fama da matsananciyar wahala da yunwa. A cikin sakon sa na barka da sallah, ya yi kira ga shugabanni da su dauki matakan rage radadin tattalin arziki bayan Ramadan.
Atiku ya yi nuni da cewa Ramadan na da mahimmanci wajen karfafa wa Musulmi kyautatawa da taimakon mabukata, don haka yana da kyau a ci gaba da irin wannan al’adar bayan azumi. Ya kuma jaddada cewa gwamnati ya kamata ta mayar da hankali wajen inganta rayuwar talakawa da rage radadin hauhawar farashin kayayyaki.
A karshe, Atiku ya bukaci al’ummar Najeriya da su hada kai domin magance matsalolin da ke hana ci gaban kasa, yana mai cewa hadin kai da zaman lafiya ne za su taimaka wajen ciyar da kasa gaba.