
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya taya al’ummar Musulmi murnar sallar azumi tare da kira ga hadin kai da tausayi. A cikin sanarwa, gwamnan ya bayyana alhinin sa kan kisan da aka yi wa wasu ‘yan asalin Kano a Jihar Edo, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta biya diyyar mutanen da aka kashe.
Gwamnan ya bayyana cewa an kafa tawaga ta musamman da za ta tafi daga Kano zuwa Edo domin tattaunawa da al’ummar Hausawa a jihar da kuma gwamnan Edo kan wannan lamari. Ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mummunan aiki.
Abba Kabir ya yi kira ga al’ummar Kano da su yi hakuri da juna, tare da karfafa zaman lafiya a cikin al’umma. Ya bayyana cewa hadin kai da zaman lafiya tsakanin kabilu da addinai daban-daban shi ne abin da ke kara daukakar Kano.
A halin yanzu, rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da kama mutane 14 da ake zargi da kisan Hausawa a Edo, tana kuma kira ga al’umma da su kaucewa daukar doka a hannu.