
‘yan Arewa sun gabatar da bukatu guda bakwai ga shugaban kasa Bola Tinubu da gwamna na jihar Edo, kan kisan matafiya Hausawa da aka yi a jihar. Lauya mai kare hakkin dan Adam, Barista Abba Hikima, ya bayyana bukatar a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook.
1. Fitar da Bayani: Gwamnati ta fitar da cikakken bayani kan adadin mutanen da aka kashe, jikkata, ko asarar dukiya a Edo.
2. Kamawa da Hukunta Masu Laifi: A gaggauta kama da hukunta duk masu hannu a wannan kisan, musamman ‘yan banga.
3. Samar da Kotu ta Musamman: A samar da kotu ta musamman don gudanar da shari’a cikin gaggawa ga wadanda suka aikata kisan.
4. Biyan Diyya: Gwamnati ta biya diyya ga iyalan wadanda aka kashe tare da basu hakuri a hukumance.
5. Kara Jami’an Tsaro: A kara samar da jami’an tsaro a yankunan Kudu domin kare matafiya da dukiyoyinsu.
6. Sabuwar Doka: A samar da sabuwar doka da za ta tsaurara hukunci kan masu daukar doka a hannu.
7. Kafa Kwamitin Bincike: A kafa kwamitin bincike na musamman da zai kunshi wakilan Arewa domin tabbatar da an yi adalci.
Bincike ya nuna cewa wasu matasa sun dauki doka a hannunsu, inda suka kashe wasu matafiya ba tare da sahihin bincike ba. Wannan lamari ya janyo fargaba a tsakanin al’umma, musamman a Arewa, wanda ya sa hukumomi ke bukatar daukar matakan gaggawa.
Barista Abba Hikima ya bayyana cewa, “Gwamnati na da alhakin tabbatar da adalci ta hanyar bincike da hukunta duk wadanda ke da hannu a wannan kisan.” Kamar yadda aka bayyana, wannan yana da matukar muhimmanci domin hana faruwar irin wannan lamari a nan gaba.