
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta bayyana damuwarta game da kisan matafiya ‘yan Arewacin Najeriya a jihar Edo, wanda ya faru a garin Uromi. A cikin sanarwa da shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya fitar, kungiyar ta yi kira ga hukumomi da su gudanar da bincike a kan lamarin tare da hukunta wadanda suka aikata wannan kisan.
Kisan ya faru ne a ranar Alhamis 27 ga watan Maris, 2025, lokacin da wasu matafiya daga jihar Rivers ke kan hanyarsu ta komawa gida don sallah. An tare su ne da wasu bata gari suka hallaka su. Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan siyasa, kungiyoyi, da malaman addini a Arewa, inda suke kira ga hukumomi su dauki mataki.
Kungiyar ta yi Allah wadai da wannan mummunan al’amari, tana mai cewa barin hakan ba tare da hukunci ba zai kara tabarbarewar tsaro a Najeriya. Gwamnonin Arewa, ciki har da Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai cewa yana da matukar muhimmanci a gudanar da bincike da hukunta masu laifi don dakile faruwar irin wannan a gaba.
JIBWIS ta jajanta wa iyalan mamatan, tare da yi musu addu’ar samun rahama a gobe kiyama.