Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Mataki Kan Tsadar Kuɗin Datar MTN da Airtel

Majalisar Dattawa ta Najeriya ta yanke shawarar gudanar da bincike kan tsadar datar kamfanonin sadarwa, musamman MTN da Airtel. Wannan mataki ya biyo bayan korafin da ƴan Najeriya ke yi kan tsadar datar da aka samu a ƙasar.

A cikin zaman Majalisar na ranar Laraba, 26 ga Maris, 2025, Sanata Asuquo Ekpenyong (Kuros Riba ta Kudu) ya gabatar da kudirin da ya jaddada bukatar a duba karin farashin data da aka yi. Majalisar ta umarci ministan sadarwa ya kira kamfanonin domin tattaunawa kan yadda za a rage farashin data daidai da ikon ƴan Najeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa karin farashin da ya kai sama da kashi 200% ya yi matuƙar shafar miliyoyin ƴan Najeriya, musamman matasan da ke dogaro da intanet wajen samun kudin shiga. Majalisar ta kuma umarci Kwamitin Sadarwa da ya bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a bi don samar da mafita mai dorewa ga wannan matsala.

Wannan mataki na Majalisar yana da nufin inganta tsarin sadarwa a Najeriya, tare da magance matsalolin da suka jawo tsadar data, kamar rashin wadatacciyar hanyar sadarwa da matsalolin wutar lantarki. Majalisar ta bukaci gwamnatin tarayya ta tattauna da kamfanonin sadarwa domin duba tsarin farashin data da tabbatar da rage shi.

Kudurin ya kuma yi nuni da bukatar rajistar ƴan kasa, wanda zai taimaka wajen tantance ƴan Najeriya ta hanyar rushe tsohuwar dokar Hukumar Kula da Shaidar Dan Kasa (NIMC) tare da kafa sabuwa.