
Sheikh Isa Ali Pantami ya yi kira ga shugabannin siyasa da su tabbatar da adalci ga al’ummar da suke mulka. Malamin ya bayyana cewa taimakon al’umma ba alfarma ba ne, yana mai cewa ya kamata shugabanni su duba yadda za su taimaka wa jama’a a cikin halin kunci da ake ciki.
Farfesa Pantami ya yi wannan jawabin a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin Karatuttukan Malaman Musulunci. Ya bayyana cewa rashin tsaro da wahalar rayuwa suna da matukar tasiri, musamman a Arewa, inda duk da kasancewar yankin da aka fi samun noma, mutane na fama da yunwa.
Ya soki tsarin raba abinci ga talakawa, yana mai cewa ya kamata a koyar da su dogaro da kai maimakon zama bara. Pantami ya ce raba abinci ba zai magance matsalolin da ke fuskantar al’umma ba, yana mai cewa ya kamata a gina al’umma domin su iya dogaro da kansu.
Malamin ya kuma ja hankalin shugabanni cewa duk wanda ya tausayawa talakawa, Allah zai saukaka masa, yayin da duk wanda ya tsananta, Allah zai tsananta masa. Wannan jawabi ya jawo hankalin mutane da dama, suna jaddada bukatar inganta rayuwar al’umma a Najeriya.