
Daruruwan mutanen Kogi ta Tsakiya sun fito zanga-zanga a tituna domin nuna goyon bayansu ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan. Zanga-zangar ta taso ne a cikin yanayi na adawa da shirin da wasu ke yi na yi wa Natasha kiranye daga majalisar dattawa.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa ƙoƙarin raba Sanata Natasha daga kujerarta na da alaƙa da wasu masu ruwa da tsaki da suka karɓi kuɗi. Sun ɗauki alluna masu ɗauke da saƙonnin kamar “Natasha, alfaharin Kogi ta Tsakiya” da “Muna tare da Natasha,” suna nuna goyon bayansu ga wakilarsu.
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Natasha a ranar 6 ga watan Maris bisa zargin rashin ɗa’a, wanda ya jawo cece-kuce a tsakanin al’ummar yankin. A cikin zanga-zangar, magoya bayan Natasha sun yi waƙoƙi a harshen Ebira, suna bayyana cewa suna tare da ita a wannan lokaci mai wahala.
A ranar Alhamis, babbar kotun tarayya ta bayar da umarnin dakatar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) daga karɓa ko aiki da kowace takardar koke da ke neman yi wa Natasha kiranye. Duk da haka, a ranar Juma’a, kotun ta soke wannan umarni, tana mai cewa ’yan ƙasa na da haƙƙin yin kiranye ga duk wani ɗan majalisa idan suna buƙatar hakan.
Sanata Natasha ta ci gaba da zargin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da cin zarafinta, inda ta bayyana cewa ta fuskanci matsaloli saboda zarginta. Wannan al’amari ya jawo hankali sosai a tsakanin al’ummar Kogi, inda mutane ke ci gaba da bayyana goyon bayansu ga Sanata Natasha.