Zargin Karbar Cin Hanci: Dan Majalisa Ya Musanta

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Gwaram a jihar Jigawa, Yusuf Shittu Galambi, ya yi magana kan zargin karbar cin hanci da ake yi wa ‘yan majalisar don amincewa da dokar ta baci a jihar Rivers.

Yusuf Shittu Galambi ya bayyana cewa rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai na ƙarya ne, yana mai cewa ba a ba su cin hanci ba kafin su amince da wannan mataki na shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

A cikin sanarwar da ya fitar, Galambi ya musanta zargin cewa an yi wa ‘yan majalisa tayin kuɗi ko kuma an matsa musu lamba don su amince da dokar ta baci. Ya ce, yawancin ‘yan majalisar sun goyi bayan wannan mataki ne saboda kishin dimokuradiyya da kuma muradun al’ummar jihar Rivers.

Galambi ya jaddada cewa shawarar da majalisar tarayya ta yanke ta dogara ne akan haɗin kan ‘yan siyasa da kuma kare tsare-tsaren dimokuradiyya. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su fahimci rawar da majalisar tarayya ke takawa wajen neman zaman lafiya da sulhu a tsakanin al’umma.

Wannan furucin ya zo ne a daidai lokacin da ake ce-ce-ku-ce kan dokar ta baci, inda wasu ƙungiyoyi ke zargin cewa an ba majalisar cin hanci don su goyi bayan wannan mataki.

Yusuf Shittu Galambi ya ƙara da cewa, “Muna goyon bayan ƙoƙarin shugaban ƙasa na ceton dimokuradiyya da kuma kare Gwamna Siminalayi Fubara, wanda ke fuskantar matsin lamba daga wasu mambobin majalisar dokokin jihar Rivers.”

Wannan jawabi ya jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan dokar ta baci a jihar Rivers.