
A ranar Jumma’a, Maris 21, 2025, karamin Ministan gidaje da raya karkara, Yusuf Ata, ya bayyana cewa yunkurin kawancen adawa tsakanin tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, da tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi ba zai yi tasiri a zabe mai zuwa ba.
Yusuf Ata ya yi wannan bayani a yayin wata taro da ya gudana a Kano, inda ya bayyana cewa duk wani yunkuri na ‘yan adawa domin kalubalantar mulkin Bola Ahmed Tinubu ba zai iya jawo wani canji ba. Ya jaddada cewa ayyukan Tinubu, ciki har da sanya dokar ta baci a jihar Ribas, sun nuna kwarewar shugabancin da ya ke da shi.
Ministan ya ce: “Kasar nan ta wuce zamanin gwaji a shugabanci, kuma ‘yan siyasar da ba su da wata manufa face amfani da tunzura jama’a ba za su samu goyon baya ba.” Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali kan kawo ci gaba mai ma’ana da kuma tabbatar da zaman lafiya a Najeriya.
Yusuf Ata ya kuma yi suka ga hadin gwiwar ‘yan adawa, yana mai cewa wannan kawance ba ta da tushe, kuma ba za ta sami karbuwa a idon ‘yan Najeriya ba. Ya bayyana cewa Tinubu ne shugaban da ya fi adalci da gaskiya a wannan lokaci, yana mai cewa gwamnatin yanzu na kan hanya madaidaiciya wajan inganta Najeriya.
A karshe, Ata ya shawarci ‘yan adawa da su farka daga barcin siyasar su, domin kuwa Najeriya na bukatar shugabanni masu nagarta da zasu kawo canji na gaskiya.