
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana rashin amincewarsa da matakin Shugaba Bola Tinubu na dakatar da Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, da sauran shugabannin jihar. Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake bayyana ra’ayinsa kan dokar ta-baci da aka ayyana a jihar, inda ya ce wannan mataki ba shi da tushe a kundin tsarin mulki.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso ya ce matakin Tinubu na dakatar da Fubara yana iya zama barazana ga tsarin dimokuradiyya da Najeriya ta gina tun daga shekarar 1999. Ya kuma karfafa gwiwar ‘yan majalisa da su daina zama ‘yar-amshin shata ga bangaren zartarwa, yana mai cewa hakan na iya haddasa tarnaki ga dimokuradiyya.
Kwankwaso ya jaddada cewa wajibi ne a tsaya kan gaskiya wajen yanke hukunci, ba tare da wata tsangwama ko biyayya ga gwamnatin da ke mulki ba. Ya kuma ce shigar da sojoji cikin harkokin mulkin jihar Ribas wani babban kuskure ne da zai iya barazana ga tsarin dimokuradiyya.
Tsohon gwamnan ya tunatar da yadda Olusegun Obasanjo ya hana sojoji shiga harkokin siyasa a lokacin mulkinsa. Kwankwaso ya yi kira ga Shugaba Tinubu da ya duba matakin da ya dauka kan lamarin Ribas domin ba wa dimokuradiyya damar ci gaba da gudana yadda ya kamata.
Gwamnatin Fubara ta yi Allah wadai da matakin da Tinubu ya dauka, inda ta bayyana cewa idan akwai wanda ya kamata a dakatar, to shi ne Ministan Abuja, Nyesom Wike. Wannan lamari ya janyo cece-kuce a fagen siyasa, tare da jaddada bukatar a duba yadda ake gudanar da mulkin jihar.