
Cif Anabs Sara-Igbe, ɗan gwagwarmaya daga yankin Neja Delta, ya bayyana fargabarsa kan halin da Gwamna Siminalayi Fubara yake ciki, kwanaki biyu bayan an dakatar da shi daga muƙaminsa. Cif Sara-Igbe ya nuna cewa har yanzu ba a ji daga gwamnan ba, wanda ya sa mutane da dama a jihar ke cikin damuwa.
A cewarsa, bayan dakatar da Fubara, an ga shi tare da iyalansa da jami’an tsaronsa suna barin gidan gwamnatin jihar, amma daga nan, ba a san inda ya tafi ba. “Muna cikin fargaba saboda ba mu ga Fubara ba, kuma babu wanda ya samu damar yin magana da shi,” in ji Sara-Igbe. Ya kuma bayyana cewa rayuwar gwamnan na cikin haɗari.
Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, saboda rikicin siyasa da ya ta’azzara a jihar. Wannan mataki ya jawo karuwar damuwa a tsakanin al’ummar jihar, inda Cif Sara-Igbe ya yi kira ga ƴan Najeriya da su fito su nuna adawa da wannan dakatarwar da ya kira ta ɓacin.
“Idan ƴan Najeriya suka yi shiru suka bar wannan abu ya faru, to zai faru a sauran wurare,” in ji shi. Hakanan, majalisar wakilan Najeriya ta amince da dokar ta ɓacin da Shugaba Tinubu ya sanya a jihar Rivers, wanda ke haifar da ƙarin fargaba a tsakanin al’umma.
Duk da kokarin da shugabannin jihar ke yi na tuntuɓar Gwamna Fubara, har yanzu ba su sami nasara ba. Al’ummar jihar na fatan samun sahihan bayanai kan inda gwamnan yake da kuma lafiyarsa.