
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin bayar da tallafi ga sabon gwamnan rikon kwarya na jihar Rivers daga asusun tarayya. Ministan shari’a, Lateef Fagbemi, ya yi wannan sanarwa yayin taron manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Fagbemi ya bayyana cewa, idan sabon gwamnan ya nemi kuɗi daga gwamnatin tarayya, za a ba shi tallafin da ya dace. Wannan mataki na gwamnatin tarayya na zuwa ne a lokacin da aka sanya dokar ta-ɓaci a jihar, domin hana faruwar rikice-rikice da ke addabar jihar mai arziƙin man fetur.
Ministan ya kare matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka, yana mai cewa ya kamata a dauki matakan da suka dace kafin a kai ga mummunan yanayi. Ya ce, “Mun shafe kusan shekaru biyu da wannan gwamnati ke mulki a jihar Rivers. Yana da mahimmanci a yi amfani da wannan dama don dawo da doka da oda.”
Haka zalika, ministan tsaro, Bello Matawalle, ya goyi bayan wannan mataki, yana mai cewa sojojin Najeriya suna cikin shirin kare muhimman kayayyakin gwamnati a jihar.
Gwamnatin tarayya ta yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa su haɗa kai domin shawo kan rikicin da ke faruwa a jihar. Wannan mataki na gwamnatin tarayya na nuna yadda ake kokarin kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Rivers.