
Wasu masu ra’ayin kare dimokuraɗiyya sun gudanar da zanga-zanga a babban birnin tarayya Abuja, domin nuna rashin jin dadinsu game da rikicin shari’a da ke faruwa a jihar Benue. Masu zanga-zangar sun yi wannan ne daga majalisar tarayya zuwa Kotun Koli, suna neman a magance matsalolin da suka taso.
Zanga-zangar ta kasance cikin lumana, inda masu zanga-zangar, wadanda suka hada da ƙungiyoyi na farar hula da kuma ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, suka rika dauke da kwalaye da rubuce-rubuce suna sukar wani shiri da aka yi na maida zaman kotun sauraron ƙarar zaɓen ƙananan hukumomin Benue daga Makurdi zuwa Abuja.
Jagoran masu zanga-zangar, Igwe Ude-Umanta, ya bayyana cewa suna neman mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun ta gaggauta shiga lamarin kuma ta kawar da alƙalai masu cin hanci daga ɓangaren shari’a. Haka kuma, sun yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya dauki matakin gaggawa domin tabbatar da an yi adalci.
Masu zanga-zangar sun bayyana cewa, “Dimokuradiyyarmu tana cikin hatsari, kuma dole ne mai shari’a ta ceto ta.” Sun kuma yi Allah-wadai da halin da ake ciki a jihar Benue, inda suka ce masu shigar da ƙarar ba su ma shiga cikin tsarin zaɓen ba.
A halin yanzu, babban alƙalin jihar Benue, mai shari’a Maurice Ikpembese, ya ba da umarnin mayar da zaman kotun daga Abuja zuwa Makurdi saboda dalilai na tsaro. Duk da haka, zanga-zangar ta nuna cewa akwai bukatar a yi wa tsarin shari’a na Najeriya gyara, don tabbatar da adalci da gaskiya a cikin harkokin zabe.