
Hukumomin tsaron Najeriya, DSS da NIA, sun fara bincike kan halartar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a taron kungiyar Majalisun Duniya (IPU) da aka gudanar ba tare da sahalewar gwamnatin Najeriya ba.
Binciken na neman gano yadda Sanata Natasha ta sami damar halartar taron, wanda aka gudanar a ranar 11 ga Maris, da kuma ko ta karya dokokin IPU da na majalisar dokokin Najeriya. Hukumomin tsaron na nazarin ko akwai wani wanda ya taimaka mata wajen shiga taron ba tare da izini ba.
Ana zargin Sanata Natasha da karya dokokin majalisar, inda shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce an dakatar da ita ne bisa zargin yin magana ba tare da izini ba. Sanatar ta bayyana cewa an yi mata dakatarwa don hana ta bayyana wasu laifuffuka da suka shafi shugabancin majalisar.
A wajen taron IPU, Sanata Natasha ta yi jawabi kan dakatarwar da aka yi mata, inda ta jaddada cewa an yi hakan ne domin hana ta bayyana gaskiya. Hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin mambobin kungiyar, inda shugaban IPU, Tulia Ackson, ta ce za a binciki batun tare da bai wa majalisar dattawan Najeriya damar kare kanta.
Haka zalika, wasu ‘yan majalisar sun musanta ikirarin Sanata Natasha, suna mai cewa an dakatar da ita ne bisa dalilin karya dokokin majalisa, ba wai saboda zarge-zargen da ta yi ba.
Binciken DSS da NIA na ci gaba, inda suke nazarin ko Sanata Natasha ta samu takardun bogi ko wani shiri na cin zarafin gwamnati. Wannan lamari na kara jawo hankali wajen batutuwan tsaro da mulkin dimokuradiyya a Najeriya.