Hukuncin Kotun Daukaka Ƙara: An bayyana Sarki sakanin Sanusi Lamido da Aminu Ado Bayero

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta bayyana Aminu Ado Bayero a matsayin sahihin Sarkin Kano, bayan hukuncin da ta yi kan rigimar sarautar da ta shafi shi da Muhammadu Sanusi II. Wannan hukuncin ya zo ne a matsayin umarni ga kowane ɓangare da ya koma matsayinsa na usuli.

Baffa Babba Ɗan’agundi, jagoran masu kara, ya bayyana cewa hukuncin kotun na nufin Aminu Ado Bayero ne halastaccen sarkin Kano. Ya bukaci hukumomin tsaro, ciki har da ƴan sanda da DSS, su tabbatar da an bi wannan hukunci yadda ya kamata.

A cikin hukuncin da Mai Shari’a Okon Abang ya yanke, kotun ta dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yi a ranar 10 ga watan Janairu, wanda ya tabbatar da maida Sanusi II kan sarauta. Wannan hukunci yana nufin cewa Aminu Ado Bayero zai ci gaba da jagorantar masarautar Kano har yanzu.

Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa hukuncin kotun ya rushe sabuwar dokar masarautar Kano ta 2024, wacce ta dawo da Sanusi II kan sarautar. A cewarsa, “Daga yau, Mai martaba sarki, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan masarautu huɗu na Kano, su ne halastattun sarakunanmu.”

Hukuncin na kotun ya jaddada cewa kowane ɓangare ya tsaya a matsayinsa, wanda hakan zai taimaka wajen kawo karshen rigimar da ta dade tana gudana a masarautar Kano. Wannan sabuwar ci gaban na nuni da cewa Aminu Ado Bayero zai ci gaba da rike mulkin sarautar Kano bisa ga hukuncin kotu.