
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta amince da wani muhimmin kudiri da ya shafi dakarun soja, wanda ke nufin cire harajin kudin shiga daga albashin su. Wannan kudiri an gabatar da shi ta hannun Kwamitin Kudi na majalisar, wanda shugaban sa, Abiodun Faleke, ya bayyana a lokacin da ake nazarin dokokin haraji da Shugaba Bola Tinubu ya mika ga majalisar.
Faleke ya jaddada cewa cire harajin na da matukar muhimmanci domin girmama aikin da sojoji ke yi wajen kare lafiyar kasa. Ya bayyana cewa wannan mataki na kwamitin ya samu goyon bayan dukkan ‘yan majalisar ba tare da wata gardama ba, saboda irin kokarin da sojojin ke yi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
A yayin taron, Faleke ya ce:
“Mai girma, kajakin majalisa da yan uwana a wannan wuri, kwamitinmu ya gabatar da kudiri kan cire haraji daga kudin shiga da dakarun sojoji. Wannan na daga cikin mutunta irin kokarin da suke yi a aikinsu.”
Wannan shawara ta kwamitin na cire haraji daga albashin sojoji na zuwa ne a lokacin da majalisar ke aiki kan sabbin dokokin haraji guda hudu da Shugaba Tinubu ya turawa majalisar tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata.
Majalisar za ta ci gaba da nazarin wannan kudiri, tare da duba ra’ayoyin jama’a domin tabbatar da cewa an yi wa dakarun soja adalci. Wannan mataki na majalisar na nuni da yadda aka dauki matakin da ya dace tare da girmama aikin sojojin Najeriya a wannan lokaci na kalubale.