EFCC Ta Bayyana Yadda Ta Yi Amfani da Naira Biliyan 50 Da Ta Kwato

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta bayyana cewa ta ƙwato Naira biliyan 50 daga hannun masu laifi a shekarar 2024, kuma ta sanya wannan kuɗi a asusun ba da lamunin karatu na ƙasa, wanda aka sani da NELFUND.

A cikin wani rahoto da hukumar ta fitar, EFCC ta bayyana cewa wannan shekarar ta kasance mafi nasara a tarihin ta tun bayan kafuwarta a 2003. Wannan nasara ta samo asali ne daga jajircewar jami’an hukumar da kuma kyakkyawan yanayin aiki da suke ciki.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa Naira biliyan 50 da aka kwato daga hannun ɓarayin gwamnati da masu aikata zamba, an zuba su ne a NELFUND domin tallafawa dalibai wajen samun ilimi. Wannan shiri na NELFUND an kafa shi ne bisa ga dokar da Shugaba Bola Tinubu ya rattaɓa a ranar 3 ga watan Afrilu, 2024.

EFCC ta bayyana cewa ta hanyar wannan shiri, za a ba wa dalibai damar samun lamuni don kammala karatunsu, wanda hakan zai taimaka wajen inganta ilimi a Najeriya. Hukumar ta kara da cewa wannan mataki na tabbatar da cewa kuɗaɗen da aka kwato suna amfanar da jama’a kai tsaye.

Hukumar ta kuma bayyana niyyar ta na ci gaba da inganta dabarun ƙwato dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya tare da yin aiki tare da hukumomi da ƙasashen duniya. Wannan yana nuna jajircewar EFCC wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.