
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya bayyana damuwarsa sakamakon kisan da aka yi wa Rabaran Sylvester Okechukwu, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Kaduna. An sace malamin a ranar 4 ga Maris, 2025, kuma an kashe shi a safiyar ranar 5 ga Maris.
A cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar, Amurka ta yi Allah wadai da wannan mummunan aiki, inda ta bayyana cewa kisan ya kasance abin takaici da rashin imani. Sun yi kira ga hukumomi da su tabbatar da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki domin ganin adalci.
Rabaran Okechukwu, malamin cocin Katolika na Tachira a Karamar Hukumar Kaura, ya shiga hannun ‘yan bindiga daga gidansa. Sanarwar daga sakataren cocin Katolika na Kafanchan, Jacob Shanet, ta tabbatar da cewa an kashe shi a cikin wata muhimmiyar rana ga mabiyan addinin Kirista.
Amurka ta mika ta’aziyyarta ga iyalan Rabaran da mabiyansa, tana mai cewa suna tare da su a wannan lokaci na alhini. Haka zalika, sun yi kira ga hukumomi da su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron al’umma da kuma kare rayukan masu ibada.
Wannan lamarin ya jawo hankali a tsakanin al’ummar Najeriya, inda ya kara bayyana kalubale da tsaro a cikin kasar. Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa suna gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata kisan.