Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Hukuncin Kotun Koli Kan Ƴan Majalisa 27: Babu Shaida Ta Sauya Sheka

Kotun Koli ta Najeriya ta yanke hukunci game da taƙaddamar sauya shekar ƴan majalisa 27 na Majalisar Dokokin Jihar Rivers, inda ta ce babu wata shaida da ke tabbatar da cewa sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A cikin hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun ta bayyana cewa Gwamna Siminalayi Fubara ya janye duk takardun da ya shigar a gaban babbar kotun tarayya, wanda hakan ya haifar da rashin tabbas kan zargin sauya shekar. Kotun ta ce, “Tun da babu wata hujja da ke nuna sun sauya sheka, to a bisa doka, babu wanda ya sauya sheka.”

Hukuncin na nufin cewa mambobi 27 na Majalisar Dokokin Jihar Rivers suna kan kujerunsu na yanzu, kuma dole ne a ci gaba da mutunta matsayin su. Kotun ta caccaki Gwamna Fubara bisa hargitsi da ya jawo wa majalisar, inda ta ce hakan barazana ce ga demokuraɗiyya.

Kotu ta jaddada cewa, “Dole ne a samu majalisar da ta cika ka’ida domin gudanar da kowace doka,” tana mai nuna cewa duk wani yunkuri na mulki ba tare da bangarori uku ba—bangaren zartarwa, bangaren majalisa, da bangaren shari’a—na nufin sabawa doka ne.

Hukuncin ya jaddada cewa Martin Amaewhule na nan a matsayin sahihin kakakin Majalisar dokokin jihar Rivers. Wannan hukunci na Kotun Koli na iya haifar da karin matsaloli na siyasa ga Gwamna Fubara a jihar.