Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Hukumar NSCDC Za Ta Dauki Sabbin Ma’aikata Don Karfafa Tsaro a Najeriya

Hukumar tsaro ta NSCDC ta sanar da shirin ɗaukar sababbin ma’aikata don ƙara inganta ayyukanta na tsaron gida a Najeriya. Shugaban hukumar, Ahmed Audi, ya bayyana cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wannan shiri, wanda ke nufin ɗaukar ƴan Najeriya masu halaye na gari.

Audi ya bayyana cewa za a sanar da ranar da za a fara aikin ɗaukar ma’aikatan a lokacin da ya dace. Wannan sanarwa ta fito ne yayin buɗe ofishin hukumar na ƙaramar hukumar Bwari a Abuja a ranar Laraba.

Shugaban ya kuma yabawa majalisar ƙaramar hukumar Bwari bisa gina ofishin reshen hukumar, inda ya ce wannan zai taimaka wajen inganta tsaro a yankin. Ahmed Audi ya ce hukumar tana fatan samun ma’aikata da za su iya bayar da gudummawa a fannin tsaro, musamman a cikin al’umma.

Kwamandan NSCDC na babban birnin tarayya Abuja, Olusola Odumosu, ya bayyana cewa hukumar za ta ƙara tura jami’ai da kayan aiki don inganta aikin su. Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumar da al’umma domin shawo kan matsalolin tsaro a yankin.

Hukumar NSCDC ta yi kira ga ƴan Najeriya da su shirya don wannan damar ta aiki, wanda zai ba su zarafin bayar da gudummawa wajen tabbatar da tsaro a ƙasar.