Jami’an Tsaro Sun Kawo Karshen Wani Fitaccen Dan Bindiga a Kaduna

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun yi nasarar dakile harin kwanton-bauna da ‘yan bindiga suka shirya a dajin Kwassau, inda aka kashe Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh. Dogo Saleh na daga cikin manyan masu garkuwa da mutane a yankin, kuma an kama shi a ranar 9 ga watan Janairu 2025.

Bayan kama Dogo Saleh, jami’an tsaro sun gudanar da bincike mai zurfi wanda ya kai ga wannan nasara. Ya bayyana cewa Dogo Saleh ya jagoranci garkuwa da mutane da dama a kan hanyar Lokoja-Abuja tare da wata tawaga da ta kunshi mayaka 100 dauke da manyan makamai, ciki har da bindigogi nau’in AK-47 da GPMG.

A lokacin da aka yi kokarin ceto Dogo Saleh daga hannun jami’an tsaro, ‘yan bindiga sun yi harin kwanton-bauna, wanda ya haifar da musayar wuta. Dogo Saleh ya samu raunuka masu tsanani daga harbin da abokan aikinsa suka yi masa yayin wannan rudani.

Duk da an garzaya da shi zuwa Asibitin Gwamnati da ke Kubwa, an tabbatar da mutuwarsa bayan wasu lokuta. Jami’an tsaro sun kuma sami nasarar kwato bindiga da tarin harsasai daga hannun ‘yan ta’addan yayin wannan farmaki.

Hakan na zuwa ne a yayin da jami’an tsaro ke kara karfafa sintiri a yankin Kagarko da manyan hanyoyi domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka tsere. Wannan nasara ta nuna jajircewar jami’an tsaro a yaki da ta’addanci a Najeriya.