
A cikin wani mataki na gaggawa, Majalisar Dokokin Kano ta kafa kwamitin bincike kan rushewar shagunan ‘yan kasuwa sama da 500 a kasuwar Rano, bayan korafin da ɗan majalisa mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad, ya gabatar.
Ibrahim Muhammad ya bayyana cewa rushewar shagunan ta jefa masu kasuwanci cikin mawuyacin hali, saboda sun rasa hanyoyin samun abinci da kudin shiga. Ya ce, “An jefa masu shagunan cikin mawuyacin hali bayan an raba su da inda suke samun halaliyarsu.”
Shugaban Majalisar, Rt. Hon Isma’il Falgore, ya bayar da umarnin kafa kwamitin mutum bakwai domin gudanar da bincike akan lamarin. Falgore ya ce, “Kwamitin zai binciki dalilin da ya sa aka rushe shagunan, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’ida wajen aiwatar da wannan rushewa.”
Dan majalisar ya kuma nemi a fayyace dalilin rushewar, yana mai jaddada cewa lamarin ya kamata a bincika don gano shin an ba wa ‘yan kasuwa isasshen gargadi kafin a rushe musu shagunan.
Rahotanni sun bayyana cewa rushewar shagunan ya haifar da zanga-zanga daga ‘yan kasuwa da mazauna yankin Rano, suna neman gwamnatin jihar ta biya diyya tare da samar da sabon wurin kasuwanci ga waɗanda abin ya shafa. Wannan mataki na majalisar ya jawo hankalin jama’a, inda ake sa ran za a gudanar da bincike mai inganci kan wannan lamarin.