ECOWAS Ta Kaddamar da Shirin Kawo Sabuwar Takardar Kudi a Najeriya


Kungiyar ECOWAS ta gudanar da taron majalisar haɗin gwiwar tattalin arziki karo na 11 a Abuja, inda ministocin kuɗi da gwamnonin bankunan kasashen yanki suka tattauna kan shirin samar da sabuwar takardar kudi guda. Wannan yunkuri na nufin inganta kasuwanci da tattalin arziki a tsakanin kasashen Afrika ta Yamma.

Ministan kuɗin Najeriya, Wale Edun, wanda ya jagoranci taron, ya jaddada bukatar haɗin gwiwar kasashen yanki domin tabbatar da nasarar wannan shiri. Ya ce, “Najeriya za ta ci gaba da goyon bayan samar da takardar kudin ECOWAS domin inganta tattalin arzikin yankin.”

A yayin taron, Edun ya bayyana cewa shirin na nufin cika sharuɗɗan haɗakar kuɗi guda a Afrika ta Yamma kafin shekarar 2027. Wannan sabuwar takardar kudi za ta taimaka wajen bunkasa kasuwanci da zuba jari a tsakanin kasashen kungiyar.

Duk da haka, an bayyana wasu kalubale da ECOWAS ke fuskanta, ciki har da rashin tsaro da hauhawar farashin kaya, wanda ke hana samun ci gaba cikin sauri. Edun ya yi kira ga dukkan kasashen yanki su haɗa kai domin inganta tsarin tattalin arziki da kuma samar da zaman lafiya.

Taron ya nuna cewa akwai bukatar ƙara kaimi wajen cimma burin haɗin gwiwar tattalin arziki a Afrika ta Yamma, wanda hakan zai taimaka wajen gina kyakkyawar makoma ga yankin.