Gwamna Aliyu Ya Ware Naira Miliyan 285 ga Malaman Addini a Ramadan

Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya sanar da ware Naira miliyan 285 a matsayin tallafi ga limamai, na’ibai, malamai da kungiyoyin addini, domin tallafawa al’ummomin musulmi a lokacin watan Ramadan.

Gwamna Aliyu ya bayyana cewa kowanne limamin Juma’a zai karbi buhuna biyar na masara da kuma N100,000, yayin da na’ibai za su sami buhuna uku na masara da N50,000 kowannensu. Haka zalika, manyan malamai 300 za su karɓi N200,000 kowannensu, yayin da wasu malamai 100 za su karɓi N100,000.

Da yake bayani a fadar gwamnatinsa a Sakkwato, gwamnan ya ce wannan tallafin yana da nufin rage wa shugabannin addinin musulunci matsin tattalin arziki a wannan wata mai alfarma. Ya bayyana cewa akwai bukatar tallafawa malamai da kungiyoyi domin ci gaba da karfafa addinin Musulunci a jihar.

Gwamna Aliyu ya yi kira ga malamai da al’umma da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’o’i domin samun zaman lafiya da tsaro a jihar da kasa baki daya. Ya kuma yi fatan al’umma za su yi amfani da watan Ramadan wajen hada kai da aikata alheri.

Hakan na zuwa ne a yayin da musulmi a Najeriya ke shirin fara azumi a ranar 1 ga watan Maris, 2025, idan har an ga jinjirin watan Ramadan. Wannan tallafi na gwamnan na daga cikin kokarin tabbatar da cewa al’ummar musulmi suna cikin koshin lafiya da jin dadin rayuwa a lokacin azumin.