
Tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, Reno Omokri, ya yi zargin cewa Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna, na yada ƙarya game da matakan tsaron da gwamnatin Bola Tinubu ke ɗauka a jihar.
Omokri ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta kashe shugabannin ‘yan bindiga fiye da 14, abin da ya kawo zaman lafiya a yankin Arewacin Najeriya. Ya zargi El-Rufai da kokarin kawar da al’ummar Kiristoci daga Kudancin Kaduna, amma wannan shiri na sa ya ci tura.
A cikin sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Omokri ya bayyana cewa El-Rufai yana cikin damuwa saboda gazawarsa wajen yin tasiri kan magajinsa, Sanata Uba Sani, da harkokin mulkin Kaduna. Ya yi zargin cewa a tsawon shekaru takwas da El-Rufai ya mulki Kaduna, ba a kama ko kashe wani shugaban ‘yan bindiga ba.
Omokri ya jaddada cewa a karkashin gwamnatin Tinubu, an kashe shugabannin ‘yan bindiga da suka addabi mutane, ciki har da Kachalla Ali Kawaje da Kachalla Halilu Sububu. Ya ce sakamakon wannan nasara ya kawo zaman lafiya a Kaduna.
Har ila yau, ya bayyana cewa yanzu an daina ganin hotunan manyan mutane suna ganawa da shugabannin ‘yan bindiga, wanda ya faru a lokacin mulkin El-Rufai. Ya kuma bayyana cewa an daina biyan kudin fansa ga ‘yan bindiga, maimakon haka suna kamewa da gurfanar da su a gaban kotu.
Omokri ya yi ikirarin cewa El-Rufai na jin haushin gazawarsa wajen kawar da Kiristoci daga Kudancin Kaduna, inda ya bayyana cewa ya jagoranci kisan kiyashin Kiristoci a wannan yanki. Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi watsi da ikirarin El-Rufai, yana mai cewa tsohon gwamnan na kokarin bata sunan wasu ne saboda takaicinsa.