
Kamfanin MRS ya sanar da rage farashin man fetur a dukkan gidajen man sa da ke Najeriya. Wannan mataki na rage farashin ya biyo bayan matakin da matatar Dangote ta dauka na rage farashin litar man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825.
A cikin sanarwar da MRS ta fitar ranar Alhamis, 27 ga watan Fabrairu, 2025, kamfanin ya bayyana cewa sabon farashin zai kasance kamar haka: a jihar Lagos, za a sayar da lita guda a Naira 860; a jihohin Kudu maso Yamma, za a sayar a Naira 870; a jihohin Arewa, Naira 880; yayin da a jihohin Kudu maso Gabas, farashin zai kasance Naira 890.
Ragin farashin na MRS na zuwa ne a lokacin da al’umma ke shirin shiga watan azumin Ramadan, wanda ya sa masana tattalin arziki ke ganin wannan mataki a matsayin wani sauki ga ‘yan Najeriya, musamman ma a lokacin da ake fama da hauhawar farashin kaya.
Kamfanin MRS ya yi gargadin cewa duk wani gidan mai da ya sayar da fetur a farashi sama da wanda aka ambata, ya kamata a tuntube su domin daukar mataki. Wannan matakin na rage farashin man fetur na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na farfado da tattalin arzikin kasa da rage radadin tsadar kayayyaki ga al’umma.