Kwanakin Karshe na Chief Edwin Clark: Iyalan sa Sun Bayyana Kalaman Sa na Karshe

Duniya ta yi rashin babban jagoran kudancin Najeriya, Chief Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru 97. Iyalan sa sun bayyana kalaman sa na karshe kafin ya rasu, inda ya jaddada kaunar sa ga Najeriya.

A cikin kalaman sa, Clark ya ce, “Ni dan Najeriya ne, ina son Najeriya, Najeriya ƙasar ta ce, ina alfahari da kasancewa dan Najeriya.” Wannan ya jaddada matsayin sa a matsayin jagora mai kishin ƙasa.

An samu addu’oi da  jimami daga shugaban Najeriya Bola Tinubu, tsofaffin shugabannin Najeriya kamar Olusegun Obasanjo, Goodluck Jonathan, da Atiku Abubakar, tare da shugaban majalisar dattijai, Godswil Akpabio, da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, wanda duk suka yi alhini kan rasuwar wannan mai kishin ƙasa.

Clark, wanda aka shigar da shi asibitin DIFF Medical Centre da ke Abuja, ya rasu da misalin karfe 11:45 na dare. Kafin rasuwarsa, ya bayyana cewa bai kamata a yi bakin ciki da tafiyar sa ba, sai dai ya kamata a dinga tunawa dashi.

A yayin da ya ke karɓar bakuncin mutane a gidansa, ya umurci wadanda suka zo da su ba su abinci da abin sha, yana mai cewa, “Dole ne ku ci gaba da gwagwarmaya don ganin cewa Najeriya ta zama al’umma mai kyau.” Wannan ya zama jigon maganganun sa na karshe ga wadanda ke tare da shi kafin ya tsunduma cikin rashin lafiya.