
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi jam’iyyar APC da yunkurin kwace zaɓen ƙananan hukumomi a jihar Osun ta hanyar amfani da ‘yan daba. A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Atiku ya yi ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na ƙoƙarin murƙushe tsarin dimokraɗiyya a jihar.
Atiku ya bayyana cewa APC ta ƙaddamar da farmaki kan tsarin dimokraɗiyya, inda ya nemi hukumomin tsaro su guji goyon bayan wannan yunkuri. Ya ce Najeriya na bukatar shugabanci nagari maimakon siyasar rigima da tashin hankali.
A cikin sanarwar, Atiku ya jaddada cewa a Osun, APC ta aika da ‘yan daba don ƙwace ikon ƙananan hukumomi 30, duk da cewa gwamnatin jihar ta ki daukar matakin da ya dace. Ya ce, “Idan ba saboda jarumtakar mutanen Osun ba, da dimokraɗiyya a jihar ta faɗa hannun ‘yan siyasar da ke son mulki ko ta halin kaka.”
Atiku ya jinjinawa mutanen Osun bisa jajircewarsu wajen kare dimokraɗiyya daga abin da ya kira danniya. Ya yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da aikinsu bisa doka, ba tare da bari APC ta yi amfani da su don cimma manufarta ba.
A ƙarshe, Atiku ya gargadi Tinubu da jam’iyyar APC su daina siyasar tada zaune tsaye, yana mai cewa, “Mutane na buƙatar shugabanci nagari, ba rikici da tashin hankali ba. Ba za mu kyale a tauye dimokraɗiyya ba.”