Gwamnatin Jihar Neja Ta Kaddamar da Shirin Tura Dalibai 1,000 Kasashen Waje

Gwamnatin jihar Neja ta fara tantance dalibai da zummar tura su karatu a kasashen waje a karkashin shirin tallafi na Gwamna Umaru Bago. Wannan shirin zai bai wa dalibai 1,000 daga makarantun gwamnati damar yin karatu a fannonin likitanci, injiniyanci, fasahar sadarwa da noma a kasashen Canada, China, India da Brazil.

Kakakin gwamnan, Ibrahim Balogi, ya bayyana wannan shiri a shafinsa na Facebook, yana mai cewa an riga an gudanar da jarabawar tantancewa a fannonin Turanci, Lissafi, Kimiya da Ilimin Zamantakewa. Wannan shirin na tafiya ne bisa ga ka’idojin cancanta, ba tare da nuna bambanci ba, domin bai wa matasan da suka fi hazaka damar samun ilimi mai inganci.

Kwamishinan Ilimi ta jihar Neja, Dr. Asabe Hadiza Mohammed, ta yaba da wannan shiri, tana mai cewa zai taimaka wajen bunkasa ilimi a jihar. Haka kuma, Daraktar Gyaran Makarantu da Inganta Ilimi, Hajiya Maimuna Mohammed, ta tabbatar da cewa tsarin jarabawar da aka gudanar ya dace da ka’idojin kasa da kasa.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa za a fitar da sunayen daliban da suka samu guraben karatun nan ba da jimawa ba, tare da fatan cewa wannan shiri zai inganta ilimin matasa a jihar Neja da kuma taimaka wajen ci gaban kasa baki daya.