
Sanata Ali Ndume ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da Majalisar Dokoki su gudanar da bincike kan zargin dan majalisar Amurka, Scott Perry, wanda ya ce Hukumar Bada Tallafin Raya Kasashe ta Duniya (USAID) na daukar nauyin kungiyar ta’addanci.
Sanatan, wanda ya wakilci Borno ta Kudu, ya bayyana cewa wannan zargi yana da matukar muhimmanci, kuma bai kamata gwamnatin Najeriya ta yi shiru a kansa ba. Ya bayyana cewa zargin na da nasaba da illolin da Boko Haram ta yi wa al’ummar Arewa, wanda ya kamata a duba da kyau.
A yayin da yake magana da Channels TV, Ndume ya ce, “Wajibi ne a duba wannan zargi, musamman ma ganin yadda aka dade ana zargin wasu kungiyoyin agaji da ke aiki a yankin Arewa maso Gabas suna tallafawa ayyukan ta’addanci.”
Ya jaddada cewa Boko Haram ta jefa al’umma cikin halin rashin tsaro, inda ya kawo misalan hare-haren da kungiyar ta yi a lokacin da ta tada bama-bamai a Abuja.
Ndume ya ce, hukumomin tsaro sun taba bayyana wasu daga cikin wannan zargi a baya, yana mai jaddada cewa yana da kyau a dauki mataki kan wannan al’amari. Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda wasu kungiyoyin agaji ke gudanar da ayyukansu a yankin.
Wannan kira na Ndume ya zo ne a lokacin da ake ta zanga-zangar neman karin tsaro a Arewa, da fatan za a dauki matakan da suka dace don tabbatar da zaman lafiya da tsaro a cikin al’umma.