Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Malamin Addini Ya Kashe Dalibar da Ya Hadu da Ita a Facebook

An kama wani Mai Ikirarin malamin addini mai suna AbdulRahman Bello bisa zargin kashe wata daliba, Hafsoh Lawal Yetunde, domin ya yi tsafi da ita. An bayyana cewa malamin ya hadu da dalibar a shafin Facebook, inda ya yi amfani da wata dabara don samun lambar wayarta sannan ya gayyace ta zuwa gidansa.

Rahotanni sun nuna cewa Hafsoh ta bace tun ranar 10 ga watan Fabrairu, 2025, bayan ta halarci wani bikin suna. Iyayenta sun fara damuwa bayan sun lura da shiru, wanda ya sa suka garzaya ofishin ‘yan sanda don kai rahoton batan ‘yarsu.

Bayan an kai rahoton batan, ‘yan sanda sun bi diddigin lambar wayarta, inda suka gano cewa kiran karshe da ta yi yana daga ga malamin. Da aka kama Bello, ya musanta sanin inda dalibar take, amma daga bisani ya bayyana cewa ta zo wajensa amma ta mutu sakamakon tashin cutarta ta asthma.

Duk da haka, binciken ‘yan sanda ya gano wasu sassan jikin Hafsoh a gidansa, tare da kayan aikin da aka yi amfani da su wajen kisan ta. Wannan lamarin ya tada hankali a cikin al’umma, inda aka bayyana Bello a matsayin wanda ya saba aikata irin wannan laifi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kwara, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa hakan ya zama abin takaici. Wannan lamari na bayyana matsalar tsaron al’umma da kuma bukatar daukar matakan kariya ga matasa, musamman a shafukan sada zumunta.