
A ranar Laraba, 12 ga watan Fabrairu, 2025, wasu ƴan bindiga sun tafka ta’asa a jihar Rivers inda suka yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika, Rabaran Livinus Maurice, tare da wasu mutum biyu. Lamarin ya faru ne yayin da suka dawo daga ziyara a asibiti a kan hanyar Elele-Isiokpo.
Rundunar ƴan sandan jihar Rivers ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’anta na ƙoƙarin ganin sun ceto mutanen da aka sace. Rabaran Maurice ya kasance limamin cocin St. Patrick’s Catholic da ke Isokpo a ƙaramar hukumar Ikwerre.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga shugaban cocin Katolika ta Port Harcourt, Rabaran Bernadine Anaele, an bayyana cewa an shigar da rahoton lamarin ga hukumomin tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace. An kuma yi kira ga mabiya addinin Kirista, musamman na Port Harcourt da Najeriya baki ɗaya, da su ƙara ƙaimi wajen yin addu’a domin a sako limamin da sauran mutanen da ke tare da shi.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Grace Iringe-Koko, ta yi magana kan lamarin, inda ta tabbatar da cewa ƴan sanda sun bazama domin ceto limamin da sauran mutanen da aka sace. Haka zalika, ta tabbatar da cewa rundunar za ta yi duk mai yiwuwa don cafke waɗanda suka aikata wannan laifi.
Wannan lamari na ƙara jaddada matsalar tsaro a jihar Rivers, inda ƴan bindiga ke ci gaba da tayar da hankali a tsakanin jama’a. Al’ummar yankin na fatan samun dauki daga hukumomi don magance wannan matsala ta tsaro.