Hadarin Mota Ya Jawo Rashi a Kano, Sanata Barau Ya Mika Ta’aziyya

An samu wani mummunan hadari a titin Kano-Maiduguri, wanda ya jawo mutuwar mutane 23. Hadarin ya faru ne yayin da motar ta yi birki a ƙarƙashin gada a unguwar Hotoro, inda hakan ya jawo jikkata wasu da dama.

Hukumar kiyaye hadurra ta ƙasa (FRSC) ta tabbatar da adadin mutanen da suka rasa rayukansu, inda ta bukaci direbobi da fasinjoji su kasance masu kula da dokokin hanya domin gujewa irin wannan hadari a nan gaba. Sanata Barau Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya bayyana alhininsa game da wannan lamari mai tayar da hankali, tare da mika ta’aziyya ga iyalan mamatan.

Sanata Barau ya wallafa sakon ta’aziyya a shafinsa na Facebook, inda ya ce: “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Na yi juyayin wannan hadari da ya auku a karkashin gadar Muhammadu Buhari. Allah ya jikansu da rahama, ya ba iyalansu hakuri da juriya.”

Haka zalika, Sanata Barau ya yi kira ga direbobi da su rika bin dokokin hanya, yana mai cewa wannan lamari yana tunatar da mu bukatar yin taka-tsantsan a hanya domin kare rayukan jama’a. Jama’a sun bayyana alhininsu tare da yin addu’o’i ga mamatan, suna kuma rokon gwamnati ta kara daukar matakan da zasu kare lafiyar direbobi da fasinjoji a tituna.

Wannan hadari ya jawo hankalin mutane da dama, inda aka yi kira ga hukumomi su tabbatar da wayar da kan jama’a game da muhimmancin bin dokokin tuki domin rage yawan hadurra a Najeriya.