ASUU Ta Gargadi Tinubu Kan Illar Gyaran Haraji ga Ilimi a Najeriya

Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta bayyana damuwarta game da sabuwar dokar sauya haraji da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gabatar, tana mai cewa wannan mataki na iya jawo wa ilimi koma baya daga shekarar 2030.

Farfesa Monday Igbafen, mai kula da reshen ASUU a Benin, ya yi wannan bayani a yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce gyaran harajin na da tasiri mai kyau a kan asusun TETFund, wanda ke tallafa wa jami’o’i wajen gudanar da bincike da gine-gine. Ya bayyana cewa, rage kason kudaden da aka ware wa TETFund daga 2025 zai kawo cikas ga ci gaban ilimi a Najeriya.

ASUU ta yi zargin cewa sabuwar doka za ta rage kason kudaden da ake warewa asusun TETFund zuwa kashi 50 a cikin shekara ta 2025, tare da rage kason kudaden zuwa kashi 66 daga shekarar 2027 zuwa 2029. Wannan yanayi, a cewar kungiyar, na iya jefa ilimin Najeriya cikin halin wahala.

Kungiyar ta ce ilimi dukiyar jama’a ce, don haka bai kamata gwamnati ta rage kudi ko ta lalata ilimi ba. Farfesa Igbafen ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye domin kare ilimi daga wannan barazana, yana mai jaddada cewa mutuwar TETFund daga shekarar 2030 zai jefa ilimin Najeriya cikin duhu.

ASUU ta ce a halin yanzu, gwamnatin tana fuskantar kalubale daga yarjejeniyar da aka yi a shekarar 2009, wanda har yanzu ba a warware matsalolin da suka taso daga gare ta ba. Wannan lamari na jaddada bukatar gwamnatin ta ba da fifiko ga ilimi, maimakon rage kudi a wannan fannin mai muhimmanci.

Kungiyar ta ce kashi 5 zuwa 7 na kasafin kudi da gwamnatin tarayya ke warewa ga ilimi ba ya dace, kuma ya nuna rashin kulawa da ci gaban ilimi a Najeriya. Wannan gargadi daga ASUU na nufin a sake duba wannan sabuwar doka domin tabbatar da ingancin ilimi a ƙasar.