
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhini da takaici kan gobarar tankar mai da ta faru a Dikko Junction, karamar hukumar Gurara, Jihar Neja, wanda ya yi sanadin asarar rayuka sama da 80.
Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, inda ya bayyana cewa wannan lamari abin takaici ne, kuma yana cikin abubuwan da za a iya gujewa. A sakon da mai ba shi shawara kan harkokin labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya yi kira ga jama’a da su guji zuwa wuraren da hadarin ya faru, musamman idan ya shafi motoci dauke da mai.
A yayin wannan hatsari, mutane da yawa sun taru wajen debo man fetur daga tankar da ta yi hatsari, wanda hakan ya kai ga fashewar tankar mai da ya jawo gobara. Tinubu ya umarci hukumomi da su samar da cikakken kulawar lafiya ga wadanda suka jikkata.
Shugaban ƙasa ya kuma umarci Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA) da ta fara gangamin wayar da kan jama’a a duk fadin ƙasar, domin ilmantar da su kan haɗarin da ke tattare da debo mai daga tankokin da suka yi hatsari. Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya ba iyalansu hakurin jure wannan rashi, tare da fatan samun sauƙi ga wadanda suka jikkata.
Tinubu ya yi kira ga hukumomin tsaro da na kiyaye hadurra su dauki matakan gaggawa don hana faruwar irin wannan mummunar al’amari a nan gaba. Wannan lamari ya jaddada bukatar ƙarin wayar da kan jama’a game da haɗarurruka da ke tattare da man fetur, da kuma illar hakan ga lafiyar al’umma.