
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayyana damuwarsa kan yadda kafafen yada labarai ba su isar da rahotanni masu inganci kan nasarorin da gwamnatinsa ta samu a cikin shekaru biyar da suka gabata. A yayin buɗe taron bita na kwanaki uku da ma’aikatar harkokin cikin da al’adu ta shirya a Damaturu, gwamna Buni ya bayyana cewa, duk da cimma nasarori a fannoni da dama, kamar tsaro, kiwon lafiya, ilimi, da kuma samar da ayyukan yi ga matasa da mata, ba a bayyana su yadda ya kamata ba.
Ya koka da cewa, gazawar hukumomi wajen bayar da bayanai kan nasarorin da aka samu ya sa kafafen yada labarai ba su bayar da cikakken rahoto kan abubuwan da suke faruwa a jihar. Gwamnan ya jaddada cewa, yana da muhimmanci jami’an yaɗa labarai su haɗa kai da kafafen yada labarai don yaɗa shirye-shiryen gwamnatinsa da nasarorin da ta samu.
Mai Mala Buni ya yi kira ga jami’an yaɗa labarai su kasance masu kwazo da ƙwarewa wajen sauke nauyin da ke kansu, tare da amfani da sababbin hanyoyin sadarwa da fasahohin zamani don isar da saƙo ga al’umma.
Hakanan, gwamnan ya ƙirƙiro sabuwar ma’aikatar kula da harkokin kiwon dabbobi, yana mai da hankali kan inganta harkokin kiwon dabbobi a jihar.