
A ranar Asabar, 18 ga Janairu, 2025, jami’an tsaro a jihar Katsina sun yi nasarar dakile wani harin da ƴan bindiga suka kai a ƙauyen Ruwan Doruwa, inda aka hallaka mutum bakwai daga cikin su. Wannan harin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, lokacin da wasu ƴan bindiga dauke da makamai irin su AK-47 suka yi yunƙurin kai hari.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa bayan samun kiran gaggawa daga al’umma, jami’an tsaro, ciki har da sojoji da jami’an DSS, sun gaggauta zuwa wurin da aka kai harin. A yayin artabun, jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindigan, inda suka hallaka bakwai daga cikinsu, wasu kuwa sun tsere dauke da raunuka.
Bayan kammala wannan aiki, jami’an tsaro sun ƙwato dabbobi da dama da ƴan bindigan suka sace, wanda ya haɗa da shanu 61, tumaki 44, jakuna biyu, da sauran dabbobi. Wannan nasara ta jami’an tsaro ta nuna ƙoƙarinsu na inganta tsaro a jihar Katsina da kuma tabbatar da lafiyar al’umma.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jami’an tsaro bisa ga jarumta da ƙwazon da suka nuna a yayin wannan aiki. Ya kuma bukaci al’umma da su ci gaba da bayar da goyon baya ta hanyar samar da sahihan bayanai ga jami’an tsaro, domin inganta tsaro da rage laifuka a jihar.
Hakan na zuwa ne a yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da yaki da ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuka a fadin ƙasar, tare da niyyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama’a.