
A ranar Alhamis, 16 ga watan Janairu, 2025, manyan mata daga sassa daban-daban na Najeriya sun halarci walimar bikin auren Dr. Farida Danjuma Goje da Barista Na’ima Goje a Abuja. Wannan taron ya gudana a gidan Sanata Danjuma Goje, inda aka gudanar da bikin cikin kyan gani da armashi.
Tsohuwar ‘yar majalisar wakilan tarayya, Hon. Aishatu Jibrin Dukku, ta gode wa dukkan al’ummar da suka halarci taron a madadin iyayen amare, tana mai bayyana farin ciki da yadda taron ya gudana. A cikin jawabinta, ta yi addu’ar cewa Allah ya sanya wannan aure ya kasance mai albarka.
Malamai da dama sun gabatar da nasihohi ga amare, suna mai jaddada muhimmancin zaman lafiya da biyayya ga miji. Daga cikin malaman da suka yi jawabi akwai Sheikh Adamu Muhammad Dokoro, Dr. Umar Garba Dokaji, da Sheikh Tahir Alyasin. Sun tunatar da amaren kan kyawawan halaye da marigayiya Hajiya Yalwa Danjuma Goje ta yi suna a lokacin rayuwarta.
Walimar ta janyo hankalin manyan mata kamar Hajiya Turai Umaru Musa Yar’adua, tsohuwar ministan mata Hajiya Zainab Maina, da Hajiya Amina Namadi Sambo, wanda hakan ya kara armashi ga bikin. Hakanan, Hajiya Mairo Aminu Waziri Tambuwal da tsohuwar ministar mata Paulen Talen ma sun halarci wannan taron.
An kammala walimar cikin jin dadi, tare da addu’o’in samun zaman lafiya ga amare da angwaye. Mahalarta sun bayyana gamsuwarsu da yadda taron ya gudana cikin tsari da kwanciyar hankali, suna fatan Allah ya ba su zuriya mai albarka.