
Gidauniyar Ibrahim Ali Usman ta gudanar da wani babban aikin tallafi na ilimi a jihar Bauchi, inda ta raba littattafai guda 1,050,000 ga ɗalibai a yankin Bauchi ta Kudu. Wannan mataki na gidauniyar na nufin inganta harkokin ilimi da kuma tallafa wa dalibai a wannan yanki.
Shugaban Gidauniyar, Hon. Ibrahim Ali Usman, ya bayyana cewa wannan aikin tallafi zai ci gaba da kasancewa, musamman ga mata da yara, domin inganta ilimin su da rayuwarsu. Ya kuma jaddada cewa gidauniyar za ta taimaka wajen raba littattafai a kowace karamar hukuma daga cikin bakwai da ke yankin Bauchi ta Kudu, inda kowacce karamar hukuma za ta samu littattafai 150,000.
Daraktan yada labaran gidauniyar, Nuruddeen Yakubu Haske, ya tabbatar da cewa an gudanar da wannan aiki ne don inganta ilimi da kuma taimakon al’umma. Haka kuma, an karrama Hon. Ibrahim Ali Usman bisa ga gudunmawar da yake bayarwa a fannin inganta ilimi da tallafawa marasa karfi.
Wannan mataki na gidauniyar ya samu yabo daga kungiyoyi da dama, wanda hakan ya nuna yadda aikin alheri zai inganta rayuwar matasa da yara a Bauchi. Gidauniyar ta sha alwashin ci gaba da ayyukan alheri da tallafi ga al’umma, tare da rokon Allah ya ba su ƙarfi da hikima domin cimma burinsu.