Ministan Walwala Ya Bayyana Dalilin Kashe N300m a Kayan Ofis

Ministan walwala da yaƙi da talauci, Nentawe Goshwe Yilwatda, ya bayyana cewa ma’aikatar sa za ta kashe sama da N300m wajen siyo kayan ofis. Wannan bayani ya fito ne a lokacin da yake kare kasafin kuɗin ma’aikatar a shirin The Morning Show na tashar Arise TV.

Ministan ya ce, “Ma’aikatar na buƙatar waɗannan kuɗaɗen domin gudanar da gyare-gyare da kuma samar da kayan aiki ga sababbin hukumomin da aka ƙirƙiro a ƙarƙashinta.” Ya bayyana cewa hukumomin suna buƙatar kayan ofis domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Yilwatda ya ƙara da cewa kasafin kuɗin ma’aikatar na shekarar 2025 ya tanadi sama da N500bn don manyan ayyuka, ciki har da shirin ciyar da dalibai da bayar da tallafi ga mabuƙata. Ya tabbatar da cewa fiye da kaso 99% na wannan kasafin kuɗin za su kai ga talakawa kai tsaye.

Duk da haka, ministan ya amsa zarge-zargen da aka yi na kashe kuɗaɗen a halin da ake ciki, inda ya bayyana cewa akwai bukatar a gyara wuraren da aka ba ma’aikatar don inganta aikin da suke yi. Wannan mataki na minista ya jawo cece-kuce a tsakanin al’umma, yayin da wasu ke ganin cewa akwai wasu hanyoyi da za a bi don rage farashin siyan kayan ofis.