Gwamnan Zamfara Yayi Bayani Dala Dala Kan Harin Sojoji a Tungar Kara

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi karin haske game da harin da ya yi sanadiyyar kashe mutane 16 a kauyen Tungar Kara, inda ya bayyana cewa ba da gangan sojojin sama suka kai wannan hari ba. A cewarsa, sojojin sun yi kuskure ne a lokacin da suke yaƙar ƴan bindigar da suka addabi yankin.

A cikin shirin siyasa da aka gudanar a gidan talabijin na Channels TV, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ya kira sojojin sama domin su kawo ɗauki bayan samun labarin cewa ƴan bindiga sun kai hari a kauyen. Ya ce, “Ba da gangan sojoji suka kashe fararen hula ba, kuskure ne wanda aka yi a yayin yaƙar ƴan ta’adda.”

Gwamnan ya jajanta wa iyalan wadanda abin ya shafa, inda ya ce sojojin suna da niyyar kawo ƙarshen ta’addancin ƴan bindiga a Zamfara. Ya bayyana cewa, ya yi imanin cewa ƙarshen Ta’addanci a yankin na kusa, tare da fatan cewa Bello Turji, shugaban ƴan bindigar, zai fuskanci hukuncin duniya nan da nan.

Rundunar sojin sama ta musanta zargin cewa harin ya kasance na gangan, amma daga baya ta ce za ta gudanar da bincike don gano haƙiƙanin abin da ya faru. Gwamna Lawal ya ce hafsan sojojin saman Najeriya ya kafa kwamiti domin duba abin da ya faru da kuma jajantawa al’ummar da lamarin ya shafa.

Gwamnan ya ƙara da cewa yana da ƙarfin gwiwa cewa sojojin za su iya murkushe ƴan bindiga a cikin lokaci mai ɗan gajeren lokaci, yana mai cewa “kwanakin Bello Turji sun kare.” Wannan jawabi ya nuna karfin gwiwa da gwamnan ke da shi a kan shirin sojoji na tabbatar da tsaron lafiya a Zamfara.