
Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa da su duba tsarin koyarwa a makarantu, musamman wajen amfani da harshen Hausa a matsayin yaren koyarwa. Wannan kira ya fito ne a yayin taron “National Literary Colloquium” da aka gudanar a cibiyar taro ta Justice Idris Legbo Kutigi a Minna.
A cewar Gwamna Bago, ya kamata a maida Hausa yaren koyarwa a makarantun firamare da sakandare, yayin da Turanci ya kamata ya zama darasi kawai. Wannan mataki, a cewarsa, zai taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa, tare da saukaka fahimtar darussa ga dalibai.
Bago ya bayyana cewa, “Idan aka maida Hausa a matsayin yaren koyarwa, hakan zai karfafa shiga makarantu da inganta ilimi, musamman a yankunan da yara ke fuskantar kalubalen karatu.” Ya kuma yi kira ga gwamnonin Arewa su yi la’akari da wannan shawara don rage yawan yaran da ke gararamba a gari.
Har ila yau, Gwamna Bago ya yi kira ga iyaye da su ba wa ‘ya’yansu kayan karatu da littattafai masu amfani domin inganta tunaninsu. Wannan shawara ta Gwamna Bago na da matukar muhimmanci wajen inganta ilimi da al’adar karatu a Najeriya, wanda ke fuskantar kalubalen jahilci da sauran matsaloli na zamantakewa.
Gwamnatin Neja ta kuma shahara wajen shirye-shiryen tallafawa matasa da inganta al’adun karatu a fadin jihar, tare da niyyar hada wasu makarantu don koyar da sana’o’in da za su dogara da kansu.