Najeriya Ta Fara Shigo da Shinkafa daga Kasar Waje Bayan Shekaru 10

Najeriya ta karbi tan 32,000 na shinkafa daga Thailand, wanda shine shigo da shinkafa na farko cikin shekaru 10. Wannan mataki na nufin rage hauhawar farashin abinci a kasar, wanda ya kai 41% a watan Mayu.

Ministan Noma, Abubakar Kyari, ya bayyana cewa gwamnati za ta ba da damar shigo da hatsi ba tare da biyan haraji ba na tsawon kwanaki 180. Wannan mataki na sassaucin haraji ya biyo bayan bukatar rage farashin abinci da ya addabi jama’a.

Kamfanin DUCAT ne ya gudanar da jigilar shinkafar daga Thailand, inda shugaban kamfanin, Adrian Beciri, ya bayyana cewa Najeriya na aiki tukuru wajen inganta damar samun abinci ga ‘yan kasa. Duk da wannan shigo da shinkafa, akwai fargabar cewa hakan na iya rage kasuwar manoman cikin gida.

Gwamnatin Najeriya na fuskantar matsalolin hauhawar farashi da suka biyo bayan sabbin matakan tattalin arziki da aka fara aiwatarwa tun lokacin da shugaban kasa Bola Tinubu ya hau kujerar mulki. An bayyana cewa wannan shigo da shinkafa na iya zama wata hanya ta rage radadin hauhawar farashi ga al’umma.

Ana sa ran shinkafar za ta fara sayarwa a farashi mai sauki, inda aka bayyana cewa ana sayar da buhun shinkafa a kan farashin N40,000 a wasu jihohin kasar, ciki har da Legas, Ogun, da Kano. Gwamnati ta yi alkawarin ci gaba da daukar matakai don tabbatar da wadatar abinci a Najeriya.