Gwamnatin Tinubu Ta Yi Wa Ma’aikatan da Suka Yi Ritaya Babban Gata

Gwamnatin tarayya ta Najeriya, a karkashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta sanar da biyan ƙarin kaso 20% na kuɗaɗen fansho ga ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda hakan ya karfafa gwiwar Ƙungiyar ƴan fansho ta Najeriya (NUP). Wannan sabuwar mataki ya haɗa da ƙarin kuɗin fansho na N32,000, wanda aka amince da shi a watan Yuli 2024.

Ƙungiyar NUP ta yaba wa shugaba Tinubu bisa wannan kyautatawa, tare da bayyana cewa hakan na nuna jajircewarsa wajen tallafawa ma’aikatan da suka yi ritaya. Wannan ƙarin kaso zai fara aiki daga watan Janairun 2024, kuma an riga an fara biyan sa ga yawancin ma’aikatan da suka yi ritaya a ƙarƙashin tsarin DBS.

Shugaban NUP, Kwamared Godwin Abumisi, ya bayyana cewa wannan mataki na gwamnati yana taimakawa wajen rage matsalolin tattalin arziƙi da ma’aikatan da suka yi ritaya ke fuskanta. Hakanan, hukumar kula da tsarin fansho (PTAD) ta samu yabo saboda tabbatar da biyan kuɗen fansho akan lokaci.

Duk da haka, ƙungiyar ta nuna damuwa kan wasu matsalolin da suka shafi tsarin biyan kuɗaɗen, inda ta nemi hukumar PTAD da ta magance waɗannan matsalolin nan take. NUP ta bayyana cewa tana da kyakkyawan fata kan jajircewar gwamnatin Tinubu wajen kula da haƙƙoƙin ma’aikatan da suka yi ritaya.