Hadimin Buhari Ya Tsokaci Kan Tsarin Rage Farashin Abinci

Tsohon mai bai wa Buhari shawara, Dolapo Bright, ya bayyana cewa an yaudari Shugaba Bola Tinubu kan cewa janye harajin shigo da kayan abinci zai rage hauhawar farashi. A cikin wata hira da ya yi, ya ce hauhawar farashin man fetur da disil da ake amfani da su wajen sufuri yana da tasiri sosai wajen ƙara tsadar kayan masarufi.

Bright ya bayyana cewa matakin janye haraji ba zai yi tasiri ba saboda tsadar sufuri da sauran matsalolin tattalin arziki. Ya yi nuni da cewa kayan da ake shigo da su daga waje na zuwa ta Legas kafin a kai su jihohi, wanda hakan yana ƙara tsada.

Hauhawar farashi a Najeriya ta ƙaru tun bayan rantsar da Tinubu, inda hauhawar farashin kayan abinci ya kai 39.93% daga 32.84% a shekarar da ta gabata. Bright ya ce rashin tallafi ga manoma da tsadar kayan aiki na daga cikin abubuwan da ke haifar da wannan hauhawar farashi.

Ya ce idan gwamnati ta samar da yanayi mai kyau, manoma za su iya aiki da inganci ba tare da dogaro da gwamnati ba.